Featured
‘Yan Kwadago Sun Yi Barazanar Daukar Mataki Idan Ba’a Janye Dokar Ta-ɓaci A Kogi Ba
Kungiyar kwadago ta yi kakkausar suka kan ayyana dokar ta baci a jihar Ribas, inda ta yi gargadin cewa za a iya tilasta mata daukar kwararan matakan da za su iya kawo cikas ga harkokin tattalin arzikin kasa matukar ba a janye Dokar ta baci ba.
Wannan barazanar na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar kwadago ta Kasa NLC na jihar Ribas, Alex Agwanwor; Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Ikechukwu Onyefuru; da Shugaban Kwamitin Tattaunawa na Hadin Gwiwa (JNC), Chuku Emecheta.
Kungiyoyin kwadagon sun nuna damuwa game da lamari , tasirin tattalin arziki, da sakamakon ayyukan gwamnatin tarayya.
Kungiyar kwadagon ta bayyana ayyana dokar ta baci da kuma dakatar da zababben gwamna, Siminalayi Fubara; mataimakiyar gwamna, Ngozi Odu; da ’yan Majalisar a matsayin wadanda ba su dace ba.
A cewar shugabannin kungiyar, al’ummar jihar Ribas ne suka zabi wadannan jami’ai cikin ’yanci, kuma duk wani yunkuri na tsige su ba tare da bin tsarin mulkin kasa ba yana kawo cikas ga dimokradiyya.
Sun dage cewa dole ne a sauya irin wadannan ayyuka domin kare mutuncin tsarin dimokuradiyyar Najeriya.
Sun bayyana irin wahalhalun da dokar ta-baci ta janyo wa ma’aikatan kananan hukumomi, wadanda ba yawansu ba kuma har yanzu ba su samu albashi ba.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, hana su albashin ma’aikata ya sa su shiga mawuyacin hali na tattalin arziki, musamman a daidai lokacin da tsadar rayuwa ta yi kamari.
