Connect with us

Featured

Wani Rahoto Ya Bayyana Karfin Alaƙa Tsakanin Rasha Da China Na Barazana Ga Amurka

A dai dai lokacin da China ke ci gaba da zama babbar barazana ga Amurka ta kusan dukkan fuskoki, wani rahoton sashen binciken sirrin ya bayyana cewa ƙarfafuwar alaƙa tsakanin ƙasar ta Asiya da ƙasashe irin Rasha da kuma Korea ta Arewa babbar barazana ce ga Washington, rahoton da ke zuwa a dai dai lokacin da ake ganin yadda shugaba Donald Trump ke ƙoƙarin kyautata alaƙa da Moscow.

Rahoton bayanan sirri na shekara-shekara da Amurka ke fitarwa ya nuna cewa China na ci gaba da zama babbar barazana ga Washington a cikin kusan dukkanin lamurra kasancewarsu ƙasashe mafiya mafiya ƙarfin tattalin arziƙi da kuma ke da mabanbantan manufofi ta fuskar siyasa da tafiyarwa.

Sai dai ƙarfafuwar alaƙa tsakanin Chinar da Rasha da kuma Iran baya ga Korea ta Arewa waɗanda dukkaninsu ƙasashe ne da ke zaman doya da manja da Amurkan, na matsayin babbar barazana ga Washington ganin yadda tarin ƙasashen ke ƙoƙarin dunƙulewa waje guda ta fannoni da dama, ciki har da kasuwanci da ƙawancen tsaro, walau a ƙungiyance ko akasin haka.

Har wayau, tasirin da China ke da shi na ci gaba kange muradan Amurka musamman a nahiyar Asiya da Pacific duk da irin ƙoƙarin da tsohon shugaban Amurkan Barrack Obama ya yi a lokacin jagorancinsa na rage tasirin Beijing da ƙarfafa alaƙar Washington da wasu daga cikin ƙasashen maƙwabtanta.

Rahoton ya nuna cewa halin da ake ciki yanzu haka na ƙarfafuwar alaƙa tsakanin Rasha da China babbar barazana ce kai tsaye ga Amurka, a wani yanayi da ake ganin yadda ɓangarorin biyu ke tafiya da ra’ayi iri ɗaya a batutuwa da dama, in banda yaƙin Ukraine da har zuwa yanzu Beijing ta gaza sawa Moscow hannu a ciki, kodayake anga yadda Korea ta Arewa ke taimakawa Rashan kasancewarta mai biyayya ga China.

A baya- bayan nan gwamnatin shugaba Donald Trump na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa tsakaninta da Moscow, musamman bayan da ta sanar da shirin sassauta takunkumai kan ƙasar ta gabashin Turai baya ga sakin tarin kuɗaɗenta da ke riƙe a bankunan Washington tun bayan da ta ƙaddamar da yaƙi kan Ukraine.

Rahoton ya bayanan sirrin ya yi gargaɗin cewa, wannan ƙawance tsakanin Beijing da wasu ƙasashe da basa ga maciji da Amurka kai tsaye zai rage tasirin Washington kan batutuwa da dama a ciki da wajen ƙasar.

China na da banbancin fahimta ko kuma rikicin kai tsaye tsakaninta da Amurka kan batutuwa masu alaƙa da mamayar kasuwanci sai kuma ƴancin yankunan Taiwan da Hong Kong waɗanda har gobe Beijing ke kallo a matsayin mallakinta amma kuma Amurka ke fatan ganin sun shaƙi iskar ƴanci.

A gefe guda wata babbar barazanar da ke gaban Amurka ita ce haɗar BRICS ƙungiyar da ke ƙunshe kusan dukkanin manyan ƙasashe daga kowacce nahiya inbanda waɗanda ke haɗakar NATO ko EU ko kuma G7, kuma galibin ƙasashen da ke cikin wannan ƙasa kai tsaye basu shiri da Amurka, yayinda wasu ma ke fama da takunkuman Amurkan a kansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet