Featured
Gwamnan Kano Ya Kafa Hukumar Bunkasa Kanan Kasuwanci Da Matsakaita Da Ƙarin Hukumomi Guda Uku
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan muhimman dokoki guda huɗu da suka kafa sabbin hukumomi da nufin ƙarfafa tsarin gwamnati da samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Tofa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa davya fitar a ranar Alhamis 24 ga Afrilu 2025.
Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-Rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA).
A cewar sanarwar, waɗannan dokokin da suka zama wani ɓangare na tsarin doka a Jihar Kano, ana sa ran za su ƙarfafa ƙirƙira, tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, daidaita harkokin talla da sanya alamomi, tare da inganta kariya da ayyukan jin ƙai ga jama’a.
Gwamna Yusuf ya bayyana sanya hannun a matsayin mataki mai muhimmanci wajen cikar burin gwamnatinsa na samar da ingantacciyar taswirar Jihar Kano.
Ya jaddada cewa sabbin hukumomin za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo masu hannun jari, da aiwatar da manufofin gwamnati yadda ya kamata.
Gwamna Abba ya kuma ja kunnuwan masu shirin karya dokokin cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri, tare da tabbatar da aniyar gwamnatinsa wajen kare doka da oda.
