Featured
Iyalan Mafarautan Da Aka Yi Wa Kisan Gilla A Edo, Sun Ce Gwamnati Ba Ta Cika Alƙawarin Da Ta Yi Musu Ba
Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya da gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba.
Ayarin mafarautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla.
Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano, tare da abokansu daga ƙananan hukumomin Garko da Kibiya da Rano.
’Yan kaɗan daga cikinsu ne suka sha da ƙyar a harin na Uromi na ranar 28 ga watan Maris, wanda ya sha tofin Allah-tsine daga ɓangarori daban-daban.
’Yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutum 14 bisa zargin hannunsu a harin, a yayin da gwamnatocin jihohin Kano da kuma inda abin ya faru, suka yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace na tallafi ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.
A watan Afrilu Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sanar da kafa kwamitin bincike na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya kan lamarin.
Gwamna Okpebholo ya sanar da haka ne bayan mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci jami’an gwamnatin Kano suka yi takakkiya zuwa Edo bayan kisan da aka yi wa Kanawan.
Daga bisani Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya Kano, inda ya yi alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma majinyatan da harin ya shafa.
A nasa jawabin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci Okpebholo zuwa garin Toronkawa, ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an biya cikakken diyya ga iyalan. Ya kuma yi musu alƙawarin tallafi na kuɗaɗe da kayan abinci.
Aminiya ta tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya, wanda kuma mamba ne a kwamitin binciken, kan dalilin rashin cika alƙawuran da gwamnatin jihar ta yi wa mutanen da abin ya shafa, amma ya ƙi cewa komai.
Haka shi ma Kwamishinan Jihar Edo, Paul Ohonbamu da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan jihar, Free Itua, ba su amsa kiranmu ba ko rubutattun tambayoyin da aka tura musu.
