Featured
Gwamnan Edo Zai Ɗauki Mataki Kan Duk Kwamishinan Da Ba Ya Sanya Irin Hular Tinubu
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya gargadi kwamishinoninsa da su tabbatar suna saka irin hular da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke amfani da ita yayin da suke zuwa ofis. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake rantsar da wasu sabbin kwamishinoni a Benin, babban birnin jihar.
Okpebholo, wanda shi ma ya sanya irin hular Tinubu a wurin taron, ya jaddada cewa babu kwamishinan da zai yarda ya halarci aiki ba tare da sanya wannan hular ba idan tufafinsa na al’ada ne da ke buƙatar hula. Ya ce, “Kun ga wannan hular, ba zan yafewa duk wanda ya zo aiki ba tare da ita a kansa ba.”
Gwamnan ya bayyana cewa dokar ta shafi dukkan kwamishinoni ba tare da nuna bambanci ba, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na ɗaukar tsarin da ya dace da al’adu da salon shugabanci.
Wannan umarni na Gwamna Okpebholo ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin matakin na nuni da nuna biyayya ga Tinubu, yayin da wasu kuma ke kallon sa a matsayin wani salo na siyasa.
