Featured
Ni Na Roƙi Tinubu Akan Ya Yafewa Maryam Sanda – Mahaifin Bilyaminu Bello
Mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, mijin Maryam Sanda, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya bayyana cewa ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa Maryam afuwa, duk da cewa kotu ta yanke mata hukuncin kisa bayan an tabbatar da samunta da laifin kashe mijinta a shekarar 2017. Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda dalilai na jin ƙai da addini, domin ganin ta samu damar kula da ‘ya’yanta biyu. Ya ƙara da cewa kisa ba zai dawo da ɗansa ba, kuma ya dade da yarda da ƙaddarar Allah game da abin da ya faru.
Alhaji Bello ya bayyana cewa tun kafin ƙarewar shari’ar ya sanar da ‘yan sanda da kotu cewa ba ya son Maryam ta fuskanci gurfanarwa saboda tunanin makomar ‘ya’yansu. Ya ce ya riga ya yafe mata, yana mai roƙon gwamnati da ta dubi lamarin da idon rahama. Ya ce idan aka aiwatar da hukuncin kisa, yaran za su rasa uwa da uba, lamarin da zai iya shafar rayuwarsu gaba ɗaya.
A nasa ɓangaren, Alhaji Garba Sanda, mahaifin Maryam, ya bayyana godiya mai zurfi ga dangin Bello bisa wannan matakin na yafiya da haɗin kai. Ya bayyana shi a matsayin abin koyi na gaskiya da imani, tare da fatan wannan yafiya za ta zama hanyar sulhu da haɗin kai tsakanin iyalan biyu, musamman domin makomar yaran.
Dukkan iyalan biyu sun bayyana cewa sun zabi yafiya, tausayi da dogaro ga Allah a maimakon fushi, tare da niyyar haɗa kai wajen tarbiyyar yaran cikin yanayin soyayya da zaman lafiya, duk da girman tashin hankalin da ya wakana.
