Connect with us

Featured

Ci gaba Da Tsare DCP Abba Kyari Rashin Adalci Ne – Dalung

Kungiyar Movement for the Emancipation of Nigeria (MEN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta saki tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, tare da dakatar da shari’arsa nan da nan. Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, wanda shi ne jagoran kungiyar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata 14 ga Oktoba, yana mai cewa ci gaba da tsare Kyari ya zama babban rashin adalci, musamman bayan yafiyar shugaba ga wasu masu laifi da dama, ciki har da wadanda Kyari da tawagarsa suka kama.

A watan Maris 2022 ne hukumar NDLEA ta gurfanar da Kyari da wasu mutane shida bisa zargin hada baki wajen safarar kwayoyi mai nauyin kilo 21.35. Sai dai a makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya yafewa mutane 175, ciki har da marigayi Herbert Macaulay, marigayi Mamman Vatsa, da Maryam Sanda. Wannan yafiya ta biyo bayan shawarwarin kwamitin shugaban kasa kan bada afuwa da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ke jagoranta.

Kungiyar MEN ta ce wannan yafiyq ta nuna rashin daidaito a tsarin shari’a, domin da dama daga cikin wadanda aka yafewa suna cikin wadanda Kyari ya kama lokacin yana aiki. Kungiyar ta ce ci gaba da shari’ar Kyari “na rushe tushen doka da adalci” kuma yana nuna son kai da bambanci wajen aiwatar da afuwa. Ta yi gargadin cewa hakan na iya zama abin tsoro ga sauran jami’an tsaro masu jajircewa wajen yaki da laifuka.

MEN ta bukaci Shugaban Kasa da Babban Lauyan Kasa da su dakatar da shari’ar gaba daya tare da sakin Kyari ba tare da bata lokaci ba. Ta ce rashin yin hakan zai zama cin zarafin adalci da kuma kafa mummunan tarihi da zai iya raunana kwarin gwiwar jami’an tsaro a yaki da miyagun laifuka a Najeriya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet