Featured
Majalisar Wakilai Za Ta Shiga Tsakani Domin Sulhunta Ƙungiyar ASUU Da Gwamnatin Tarayya
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta sanar da shirin shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, bayan kungiyar ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu a ranar Litinin. Wannan mataki ya biyo bayan kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Badagry, Sesi Whinga na jam’iyyar APC ya gabatar a zaman majalisar ranar Talata 14 ga Oktoba.
Whinga ya bayyana cewa tsoma bakin majalisar na nufin samo mafita ta dindindin ga matsalolin da suka dade suna addabar tsarin ilimin jami’o’in gwamnati a kasar. ASUU ta shiga yajin aiki ne bayan karewar wa’adin gargadi na kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati, domin biya mata bukatunta da suka hada da biyan albashin da aka dakatar, aiwatar da yarjejeniyar 2009, da samar da kudaden ci gaban jami’o’i.
Sauran korafe-korafen sun hada da biyan ragowar albashi da hakkokin karin girma da aka jinkirta fiye da shekaru hudu, da sakin kudaden hadin gwiwar ma’aikata. Duk da cewa kwamitoci da dama sun yi kokarin kammala tattaunawar, an kasa aiwatar da rahoton karshe na kwamitin Yayale Ahmed tun daga watan Disamba 2024.
A halin yanzu, Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya umurci shugabannin jami’o’i da su aiwatar da dokar “ba aiki, ba biyan albashi” ga malaman da ke cikin yajin aiki. Wannan yajin aikin ya jawo tsaiko a jarrabawa a jami’o’i da dama, abin da ya sa majalisar ta dauki matakin shiga tsakani cikin gaggawa domin kaucewa dakatar da harkokin jami’o’i gaba daya.
