Connect with us

Featured

PDP Ta Mayar Da Anyanwu Matsayinsa, Ta Soke Taron NEC Na Ranar 30 Ga Yuni

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta janye matsayinta na baya dangane da Sanata Samuel Anyanwu, tare da dage taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka shirya yi ranar 30 ga Yuni, bayan yin wani taro da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Da yake magana a wani taron manema labarai a sakatariyar ƙasa ta jam’iyyar PDP da ke Abuja a ranar Laraba 25 ga Yuni, 2025. Mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa wannan mataki da suka ɗauka ya yi wahala, amma yawancin manyan shugabanni sun amince da shi.

Damagum, wanda ke tare da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da sauran jiga-jigan jam’iyyar, ya bayyana cewa PDP ta yanke shawarar mayar da Anyanwu a matsayin Sakatare na ƙasa a kwamitin zartarwa (NWC)

Ya ce, maimakon taron NEC da aka shirya, yanzu za a gudanar da wani babban taron caucus na jam’iyyar a ranar 30 ga Yuni.

PDP dai na fama da rikice-rikicen cikin gida tun bayan faduwarta daga mulki a 2015. Wadanda suka haɗa da rikicewar shugabanci, ficewar mambobi, da matsalolin ɓangaranci a wasu jihohi.

A halin yanzu, rikicin shugabanci a matsayin Sakatare na ƙasa tsakanin Sunday Udeh-Okoye da Anyanwu ne ke ci gaba da addabar jam’iyyar.

Saboda rikicin, PDP ta naɗa Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin Sakatare na ƙasa. Amma rahoton kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Taraba, Kefas Agbu, ya nuna cewa har yanzu INEC Anyanwu ta sani a matsayin sahihin Sakatare na ƙasa.

 

 

 

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet