Connect with us

Featured

A Cikin Duk Ɗalibai 10, Ana Samun 4 Da Su Ke Amfani Da Miyagun Ƙwayoyi – NDLEA

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Oyo, ta bayyana cewa kimanin dalibai hudu zuwa biyar cikin goma suna amfani da miyagun ƙwayoyi.

Kwamandan hukumar a jihar, Olayinka Joe-Fadile, ne ya bayyana hakan a Ibadan a ranar Laraba 25 ga Yuni, 2025. Yayin zanga-zangar wayar da kai da hukumar ta shirya domin bikin Ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya ta 2025.

Ana bikin wannan rana a 26 ga Yuni na kowacce shekara, Ttaken bikin bana shi ne: “Shaida Ta Bayyana: Ku Zuba Jari a fannin Rigakafi,.”

Joe-Fadile ya ce matsalar shaye-shaye na kara ta’azzara, kuma alkaluma sun nuna cewa yanzu matasa na shiga harkar ƙwayoyi tun da kananun shekarun su.

“Muna ƙara azama wajen wayar da kai a makarantu, tun daga firamare har zuwa sakandare da jami’o’i, saboda yawaitar masu amfani da ƙwayoy,” in ji shi.

“Yanzu haka muna samun yara daga shekara tara suna fara shan miyagun ƙwayoyi.

Alkaluma sun kuma nuna mana cewa kimanin dalibai hudu zuwa biyar cikin goma suna amfani da ƙwayoyi.”

Ya kuma bayyana cewa hukumar NDLEA ta kama mutane 150 bisa laifin da ke da alaka da miyagun ƙwayoyi a cikin watannin baya-bayan nan, tare da ƙone tan 11 na ƙwayoyi daban-daban da aka kama.

“Mun kuma gano cewa mutane da dama na girmama shugabannin addini, saboda haka muka yi haɗin gwiwa da su wajen isar da saƙonmu,” a cewar kwamandan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mahalarta wannan gangamin sun hada da jami’an Sojojin Najeriya, hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Kwastam, Hukumar Shige da Fice ta Kasa, da kuma matasan hidimar kasa (NYSC), da sauransu.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet