Featured
Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokokin Gyaran Haraji Guda Hudu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan sabbin dokokin gyaran haraji guda hudu da suka shafi muhimman fannoni na tsarin kuɗi da tara haraji a Najeriya.
An gudanar da bikin rattaba hannun ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja da misalin ƙarfe 3:20 na yamma a ranar Alhamis 26 ga Yuni, 2025.
Ga jerin dokokin da aka sanya wa hannu:
1. Dokar Harajin Najeriya (Nigeria Tax Bill – Ease of Doing Business)
2. Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya (Nigeria Tax Administration Bill)
3. Dokar Kafa Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (Nigeria Revenue Service Establishment Bill)
4. Dokar Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Tara Haraji (Joint Revenue Board Establishment Bill)
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ce ta amince da dokokin bayan shafe watanni ana tattaunawa da ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce:
“Da zarar an fara aiwatar da sabbin dokokin harajin, ana sa ran za su kawo sauyi mai muhimmanci a tsarin tara haraji, su ƙara yawan kudaden shiga, su kyautata yanayin kasuwanci, da kuma janyo hannun jarin cikin gida da na ƙetare.”
