Featured
Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Hallaka Ƴan Ta’adda A Jihar Neja
Dakarun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a karkashin Operation FANSAN YAMMA, sun kai hare-hare ta sama, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama a jihar Neja, domin taimakawa dakarun sojin ƙasa wajen fatattakar ƴan ta’addan da suka kai hare-hare a baya-bayan nan.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayani na hukumar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Juma’a 27 ga Yuni, 2027 a Abuja, ya ce hare-haren sun gudana ne tsakanin 24 zuwa 26 ga Yuni, 2025, bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta gano ayyukan ta’addanci da suka haɗa da hare-hare da satar shanu a kauyukan Kakihun da Kumbashi, ta hanyar haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
“Bayan samun bayanan sirri, mun tura jiragen yaƙi cikin gaggawa domin kai hare-haren ta sama, inda muka kashe ‘yan ta’adda da dama, muka lalata kayayyakin su”.
“Rundunar Sojin Sama ta Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan,” a cewar sanarwar.
