Featured
APC Ta Sanya Ranar 24 ga Yuli Domin Zaɓen Sabon Shugaban Jam’iyyar
Jam’iyyar APC za ta gudanar da taron Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) a ranar 24 ga Yuli, 2025 a Abuja, domin yanke hukunci kan ko Ali Bukar Dalori zai ci gaba da rike mukamin mukaddashin shugaban jam’iyya har zuwa babban taron jam’iyya ko kuma a zabi sabon shugaban jam’iyya na dindindin.
Wannan ya biyo bayan murabus din tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, daga shugabancin jam’iyyar a ranar Juma’a 27 ga Yuni, 2025, yana mai cewa lafiyarsa ce ta tilasta masa yin hakan.
Bayan taro da shugaban kasa, Bola Tinubu, jam’iyyar ta bayyana Dalori a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyya.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Festus Fuanter, bayan taron Kwamitin amintattu na Ƙasa (NWC) da aka gudanar a ranar Litinin 30 ga Yuni 2025 a Abuja.
Ya kuma bayyana cewa NEC ce za ta yanke hukunci kan sahihancin nadin ko zaben sabon shugaba.
Jam’iyyar ta kuma amince da murabus din Ganduje tare da yi masa fatan sauki da waraka.
Dalori ya bayyana cewa wannan nadin ba nasara ce ta kashin kansa ba, nasara ce ta kowa da kowa, kazalika zai yi aiki tukuru domin farfado da jam’iyyar da kuma karfafa hadin kai da tushe.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa shiri na musamman yana tafe domin gudanar da zaben cike gurbi a jihohi daban-daban, sakamakon rasuwar wasu ‘yan majalisa ko sauya sheka. Haka kuma, ana shirin gudanar da sabbin tarurrukan jam’iyya a matakin gundumomi, kananan hukumomi da jihohi.
Dalori ya kara da cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da goyon bayan shirin “Renewed Hope” na Shugaba Tinubu, yana mai cewa lokaci ne na hadin kai, ba rikici ko rarrabuwar kawuna ba.
