Featured
Kwankwaso Ba Zai Tsaya Takara A Jam’iyyarmu A 2027 Ba – NNPP
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana cewa tsohon dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi da damar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2027.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Agbo Major, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 05 ga Yuli, 2025.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Dr. Major ya mayar da martani ne kan kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama a NNPP kuma zai tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar a zaben 2027.
Galadima ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa jam’iyyar APC kamar yadda ake ta yadawa, inda ya kara da cewa suna nan a NNPP 2027. Inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara wa Kwankwaso baya.
A cewar Agbo “Kwankwaso da Galadima tuni an kore su daga jam’iyyar NNPP saboda ayyukan cin amanar jam’iyya da suka aikata.”
Ya kuma kara da cewa: “Kwankwaso ba zai iya amfani da jamiyyar NNPP don wani yunkurin siyasa ba, domin tuni an tsinke alaka da Kwankwasiyya Movement bayan kammala zaben 2023.”
