Connect with us

Featured

Ahmed Musa Ya Ƙudiri Aniyar Dawo Da Martabar Kano Pillars

Sabon Janar manaja na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa, ya bayyana shirin sa na ganin ya dawo da martabar kungiyar Kano Pillars a idon duniya kamar yadda aka santa a baya.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a dakin taro na Sani Abacha Stadium da ke Ƙofar Mata ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025. Ahmed Musa, MON, OON, ya bayyana irin kalubalen da ke gabansa na ganin kungiyar ta dawo hayyacinta, Musa ya ce aikin ba karami bane, amma idan ya samu goyon baya to abu ne mai sauƙi.

Musa ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki domin cimma nasara. Ya bukaci al’ummar Jihar Kano da su bayar da goyon baya da hadin kai domin ganin an samu nasara a sabuwar kakar wasa.

Babban Manajan ya nuna godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da ya yi da nada shi a matsayin wanda zai jagoranci tafiyar da al’amuran kungiyar. “Zamu dawo da Sai Masu Gida kan ganiyarta, kuma da taimakon Allah ba za mu kunyata Gwamna ba,” in ji Musa.

Ahmed Musa ya kuma bayyana jin dadin ‘yan wasa a matsayin abinda za su bawa muhimmanci, wanda hakan shi ne zai zama ginshikin nasarar kungiyar, yana mai cewa su ne ‘yan wasan da ke wakiltar Pillars. “Ba tare da jin dadin su ba, nasara ba za ta yiwu ba. Za mu tabbatar sun samu tallafi, kwarin gwiwa da kuma tsafta a fili da wajen fili,” in ji shi.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa, masu daukar nauyi da abokan hulɗa da su tallafa wa ci gaban kungiyar, yana mai tabbatar da cewa kofa a bude take ga duk masu sha’awar daukar nauyi a kungiyar.

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet