Connect with us

Featured

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Musanta Batun Fara Ɗaukar Sabbin Ma’aikata

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an fara daukar ma’aikata don horon soja na 2025/2026 (Basic Military Training Course – BMTC) da kuma Direct Short Service Commission – DSSC, tana mai bayyana saƙon a matsayin ƙarya da yaudara.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayar da Bayanai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Alhamis 17 ga Yuli 2025, rundunar ta bayyana cewa ba ta fara wani shirin daukar ma’aikata ba a halin yanzu, don haka jama’a su yi watsi da irin waɗannan saƙonni.

Sanarwar ta ce: “An jawo hankalin rundunar Sojin Sama ta Najeriya game da saƙonni na bogi da ke yawo a yanar gizo, da ke cewa NAF ta fara daukar ma’aikata don shirin horarwa na 2025/2026 BMTC da DSSC. Muna so mu fayyace cewa babu wani irin wannan shiri da ake gudanarwa a yanzu. Don haka, jama’a su yi watsi da irin waɗannan saƙonni baki ɗaya.”

Ejodame ya bayyana cewa tsarin daukar ma’aikata na NAF yana kasancewa kyauta gaba ɗaya, a bude kuma bisa cancanta, ba tare da wani caji ba. Haka kuma, rundunar ba ta amfani da wakilai ko masu shiga tsakani wajen daukar ma’aikata.

Ya ƙara da cewa duk wani sahihin batu kan daukar aiki daga NAF za a wallafa shi a jaridun ƙasa, shafin yanar gizo na NAF, da kuma sahihan kafafen sada zumunta na rundunar.

“Muna ƙara jan hankalin jama’a su guji fadawa hannun masu damfara ta yanar gizo, kuma su rika kula da irin waɗannan sanarwa da ba su fito daga hukumomi ba,” in ji shi.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet