Connect with us

Featured

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Karyata Zargin Gudanar Da Bincike Kan Shugabar ALGON

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karyata rahotannin da ke cewa tana shirin bincikar Shugabar Kungiyar Kananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar, Hajiya Sa’adatu Yusha’u, tana mai cewa rahotannin ba gaskiya ba ne.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Kakakin Majalisar, Malam Kamaluddeen Shawai, ya fitar.

Shawai ya ce rahoton da ya karade kafafen sada zumunta da yanar gizo karya ce tsagwaro, inda rahoton ya ce majalisar ta kammala shirye-shirye don bincikar Shugabar ALGON, wadda kuma ita ce Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, kan zarge-zargen da suka shafi rabon filaye ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana cewa, Shugaban Masu rinjayen na Majalisar, Hon. Lawal Hussain-Dala, bai bayar da wani bayani ko hira da kowanne kafar yada labarai ba dangane da wannan batu.

“Karɓar takardar koke daga Shugaban Masu rinjayen ba yana nufin amincewa da fara bincike ba ne, haka kuma ba yana nufin cewa majalisar ta yanke hukunci ba,” in ji Shawai.

Ya ce Majalisar ta yi Allah-wadai da yadda aka yi amfani da tsarin majalisa ba daidai ba, yana mai cewa rahotannin sun yi niyya ne kawai don bata sunan Shugaban Masu rinjaye da kuma martabar Majalisar gaba ɗaya.

Shawai ya kara da cewa Majalisar na aiki ne bisa doka da tsarin mulki, kuma duk wani bincike dole ne ya bi matakai na doka da bayar da dama ga dukkan ɓangarori su kare kansu.

“Majalisar tana da ’yancin karɓa da duba kowace takardar koke daga jama’a ko kungiyoyi, bisa tsarin gaskiya da bin doka.”

Majalisar ta bukaci wadanda suka yada rahoton da su janye shi tare da bayar da hakuri a fili cikin kwanaki bakwai, in ba haka ba za a dauki matakin shari’a a kansu.

 

NAN

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet