Featured
Watsa Naira Ko Tattakawa Babban Laifi Ne A Najeriya – Shugaban EFCC
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Mista Ola Olukoyede, ya ja kunnen ‘yan Najeriya da su daina wulakanta Naira, yana mai jaddada cewa dabi’ar watsawa ko tattake kudin ba al’ada ce mai kyau ba, kuma laifi ne a dokar kasa.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 18 ga Yuli a birnin Lagos, yayin wani taron fadakarwa da hukumar ta shirya da nufin wayar da kan al’umma.
Ya bayyana Naira a matsayin “tambarin ikon mallakar kai na kasa,” yana mai nuna damuwarsa kan yadda ake cigaba da wulakanta kudin musamman a lokutan bukukuwa inda ake yawan watsawa, liƙi ko tattake kudin.
“Babu wanda zai fita ya yi aiki sosai sannan ya fito yana watsi da su yana takawa,” a cewarsa,
Yana mai cewa irin wannan hali ba kawai laifi ba ne, hasali ma yana cutar da tattalin arzikin kasa.
Shugaban EFCC din ya kara da cewa hukumar na kara matsa lamba wajen dakile masu sayar da kudade ba bisa ka’ida ba da kuma wadanda ke raina darajar Naira.
Ya bayyana cewa suna aiki kafada da kafada da Babban Bankin Najeriya (CBN), inda suka kafa runduna ta musamman domin yaki da “Dollarization” da kuma wulakanta Naira.
Ya kuma mayar da martani kan masu sukar hukumar da cewa EFCC ta fi mayar da hankali kan manyan laifuka, inda ya ce duk wani laifi, laifi ne a dokar kasa.
