Connect with us

Featured

Ministan Jinkai Nentawe Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja. Taron wanda ke gudana a fadar shugaban ƙasar, ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam’iyyar ta APC

Kafin zaɓensa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kasance ministan jin-ƙai na Najeriya.

Sunan Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ɓulla a baya-bayan nan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ake kyautata zaton za su maye gurbin Ganduje

Tsohon malamin jami’ar ya fito ne daga jihar Filato, kuma ya koyar ne a Jami’ar ayyukan noma da ke Makurdi kafin tsunduma cikin harkokin siyasa.

Haka nan ya taɓa zama kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya tsakanin shekarun 2017 da 2021 a jihohin Benue da Anambra da Osun da Rivers da kuma Cross River.

Masu lura da al’amura na ganin sabon shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwalda ka iya zama cikakken shugaban jam’iyyar ko da bayan babban taronta na watan Disamba.

A watan Disamba ne jam’iyyar mai mulki za ta yi babban taronta na ƙasa domin zaɓen shugaban jam’iyyar mai cikakken iko.

Zaɓen Farfesa Nentawe Yilwalda a na yau Alhamis ɗaya ne daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran taron ya cimma matsaya a kai.

Hakan ya biyo bayan saukan ba-zato ba tsammani da tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje ya yi a watan Yuni.

Abdullahi Ganduje ya ce ya sauka ne bisa dalilai na ƙashin kai, musamman domin kula da lafiya.

Jim kaɗan bayan haka ne aka naɗa Ali Bukar Dalori, ɗan asalin jihar Borno a matsayin mai riƙon muƙamin.

Sai dai saukar Ganduje daga muƙamin ta zo ne bayan tsawon lokaci da mutanen arewa ta tsakiyar ƙasar suka kwashe suna neman a mayar da muƙamin zuwa yankin.

Hasali ma batun ya yi ta tayar da ƙura tun kafin miƙa wa tsohon gwamnan na Kano muƙamin da kuma bayan ya hau kujerar.

Hakan kuwa ya faru ne kasancewar tun asali muƙamin na hannun ɗan asalin yankin na arewa ta tsakiya ne, wato tsohon gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Adamu.

Tuni dai aka rantsar da Nentawe a matsayin shugaban APC nan take.

Ya ɗauki rantsuwar ofis da misalin karfe 2:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar, yayin taron da ke gudana a yau Alhamis.

 

 

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet