Connect with us

Featured

Kotu Ta Umarci NYSC Ta Bar Mata Su Riƙa Sanya Siket

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke haramcin da Hukumar Kula da Aikin Yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta sanya kan sanya siket ga mata masu yi wa kasa hidima.

A hukuncin da mai shari’a Hauwa Joseph Yilwa ta yanke, ta ce tilasta wa mata sanya wando a matsayin kayan aiki kawai ya ci karo da ‘yancinsu na addini da kimar ɗan adam, kamar yadda kundin tsarin mulki na Najeriya ya tanada.

Wasu tsofaffin ’yan yi wa kasa hidima guda biyu — Ogunjobi John Blessing da Ayuba Vivian — ne suka shigar da ƙara daban-daban bayan da NYSC ta ƙi basu takardar shaidar kammala aikin yi wa ƙasa saboda ƙin sanya wando. Kotun ta haɗa ƙarar guda biyu domin saurara tare.

Mai shari’a Yilwa ta bayyana cewa ƙin yarda da siket a matsayin ɗaya daga cikin kayan sanye-sanyen mata ya saba wa sashe na 38(1) na kundin tsarin mulki na 1999 (wanda aka gyara), da kuma Littafin Kubawar Shari’a (Deuteronomy) 22:5 a cikin Littafi Mai Tsarki.

Kotun ta kuma umarci NYSC da ta biya Naira miliyan 10 a matsayin diyya ga waɗanda suka shigar da ƙarar.

Ayuba, wadda ta kammala karatu a fannin Microbiology daga Jami’ar Kaduna a 2018, an tura ta yi aikin yi wa ƙasa a jihar Zamfara, amma ta ƙi karɓar wando da aka ba ta saboda dalilan addini.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet