Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Kori Hadimansa Biyu Saboda Shiga Harkar Belin Dillalin Miyagun Kwayoyi da Karkatar Da Tallafin Abinci

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da korar wasu manyan hadimai biyu na musamman (Senior Special Assistants – SSAs) bayan rahoton kwamitocin bincike sun tabbatar da wadanda ake zargin su aikata laifuka daban-daban.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar 09 ga Agusta, 2025.

Gwamnan ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, SSA kan Harkokin Wayar da Kai na Siyasa, bayan kwamitin bincike na musamman ya tabbatar da cewa yana da hannu a sakin dillalin miyagun kwayoyin nan Sulaiman Aminu Danwawu.

A wata wasika da aka fitar ranar Juma’a, 8 ga Agusta 2025, Sakataren Gwamnatin Jihar ya umarci Sharada da ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa ga Babban Sakataren Dindindin na Bincike, Kimantawa da Harkokin Siyasa (REPA), ofishin SSG, kafin ranar Litinin, 11 ga Agusta 2025.

Haka kuma an gargade shi da kada ya sake gabatar da kansa a matsayin jami’in gwamnati a wannan mulki.

Haka zalika, Gwamnan ya sallami Tasiu Adamu Al’amin Roba, SSA na Ofishin Majalisar Zartarwa, bayan an kama shi da laifin karkatar da hatsi na tallafin gwamnati a wani rumbun ajiya da ke Sharada a shekarar 2024.

An riga an gurfanar da Roba a kotu, inda ake tuhumarsa da sata da kuma hada baki wajen karkatar da kadarorin jama’a.

Shi ma an umurce shi da ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa, ciki har da katin shaidarsa, kafin ranar Litinin, 11 ga Agusta 2025. Haka kuma an gargade shi da kada ya kuma bayyana kansa a matsayin jami’in gwamnati a wannan gwamnati.

A wani batu mai nasaba da haka, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Magudanan Ruwa, bayan kwamitin bincike ya tabbatar da cewa ba shi da laifi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tabbatar da ladabtarwa, gaskiya da adalci, da rashin sassauci ga cin hanci da rashawa, tare da gargadin cewa dukkan jami’an gwamnati su tabbatar da bin ka’ida da gaskiya a aikinsu da rayuwarsu ta kashin kai.

Gwamnatin ta yi kira ga jama’a da kada su yi hulɗa da wadannan hadiman da aka kora kan duk wani batu da ya shafi gwamnatin jihar Kano, domin duk wanda ya yi hakan, zai dauki alhakin abin da zai biyo baya.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet