Featured
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Ya Ƙaryata Rade-radin Komawarsa jam’iyyar ADC
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 10 ga Agusta, Mustapha ya bayyana rahoton a matsayin labarin karya, inda ya jaddada cewa bai taɓa yin wata tattaunawa da ‘yan adawa ko abokan haɗin gwiwarsu ba.
Ya ce: “An jawo hankalina zuwa wani labari da ke yawo da ke danganta ni da gamayyar adawa da zaben ADC a matsayin jam’iyyarsu. Ina so jama’a su sani cewa wannan labari ne na bogi. Ba ni cikin kowace gamayyar adawa, kuma ban shiga wata tattaunawa da wadanda ke ciki ba.”
Mustapha ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin masu kafa APC, inda ya ce ba zai iya barin jam’iyyar da ya taimaka wajen kafawa ba.
Ya kara da cewa, ko da yake APC kamar kowace jam’iyya tana da kalubale, mafita ita ce a gyara daga ciki maimakon barin ta a koma wata jam’iyya.
Daga karshe, ya roki jama’a da su yi watsi da duk wani hasashe da ke cewa ya fice daga jam’iyyar.
