Connect with us

Featured

Yanke Hukunci Kaɗai Ba Zai Kawo Ƙarshen Cin Hanci a Najeriya Ba Dole Sai An Haɗa Da Wasu Dabaru — Shugaban Hukumar ICPC

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Musa Aliyu, ya bayyana cewa amfani da hukunci kaɗai ba zai wadatar wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ba.

Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Litinin 18 ga Agusta a Maiduguri, yayin jawabin maraba a wajen taron kwana ɗaya na tattaunawa da lauyoyin gwamnati na jihohi (Attorneys-General) daga Arewa maso Gabas. Ya ce dole ne Najeriya ta haɗa hanyoyi daban-daban domin magance cin hanci.

A cewarsa, cin hanci na daga cikin manyan matsalolin da suka jima suna raunana tattalin arzikin ƙasa, haifar da rashin tsaro, da kuma ƙara lalata amincewar jama’a ga cibiyoyin gwamnati.

Ya ce: “Mun sani daga kwarewar ƙasashen duniya da kuma dokokinmu cewa hukunci kaɗai bai isa ba. Dole mu haɗa hanyoyi: dawo da dukiyar da aka sace, tabbatar da adalci ga waɗanda aka zalunta, ƙarfafa tsarinmu, kuma mu yi aiki tare a tsakanin hukumomi da yankuna.”

Ya ƙara da cewa: “’Yan uwa mahalarta, cin hanci na daga cikin manyan ƙalubalen zamaninmu. Yana raunana tattalin arziki, yana haifar da rashin tsaro, kuma yana lalata amincewar jama’a. Duniya baki ɗaya na magana da murya ɗaya kan cin hanci, kuma Najeriya bai kamata ta tsaya a baya ba.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet