Featured
Ina Fatan Sasanta Rikicin Ukraine da Russia Ya Zama Sanadin Shigata Aljannah – Trump
Shugaba Donald Trump ya yi nuni da cewa kawo ƙarshen yaƙin tsakanin Rasha da Ukraine ba wai kawai zai dakatar da ɗaya daga cikin mafi munin zubar da jini a tarihi ba, face hakan zai iya taimaka masa wajen samun shiga Aljanna.
Da yake magana a shirin Fox and Friends kwana guda bayan taron da ya yi da shugabannin Turai – ciki har da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky – a Fadar White House, Trump ya yi raha da cewa taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin na iya amfani da shi kansa da kuma siyasar sa.
“Ina ganin idan na iya ceto mutane 7,000 a kowane mako daga mutuwa, wannan babban abu ne. Ina so in yi ƙoƙari in shiga Aljanna idan zai yiwu. ” kamar yadda ya bayyana cikin barkwanci.
Wannan furucin ya zo ne yayin da Trump ke ci gaba da matsa lamba a kan tattaunawar zaman lafiya domin kawo ƙarshen yaƙin da ya shiga shekara ta huɗu tun bayan mamayar Rasha a Ukraine. Tun da farko, ya sha nuna burinsa na zama mai shiga tsakani a matsayin alkawarin kamfen da kuma abin da zai bari a tarihin mulkinsa. A ‘yan makonnin nan ma ya maimaita cewa ya cancanci lambar yabo ta Nobel Peace Prize saboda ƙoƙarinsa na rage rikice-rikicen duniya.
Sai dai duk da wannan fata, shawo kan Rasha ya kasance babban ƙalubale. A makon da ya gabata ya gana da Vladimir Putin a Alaska – ganawarsu ta farko tun 2019 – domin tattauna yiwuwar shiga tattaunawar zaman lafiya. Amma Moscow ta ƙi amincewa da tsagaita wuta nan da nan, tana jaddada cewa da bukatar Ukraine ta miƙa wasu yankuna kafin a kawo ƙarshen yaƙin.
Amurka, tare da haɗin kan ƙawayenta na Turai, sun goyi bayan kiran a dakatar da yaƙi tare da ci gaba da tattaunawa. Zelensky ya shiga zaman taron na White House a wannan mako, inda ake sa ran ci gaba da ganawa a makonni masu zuwa yayin da Washington ke matsa lamba domin samun ci gaba.
Trump, wanda yake kiran kansa Kirista mai bin addini ba tare da takamaiman tsari ba, ya sha bayyana imanin sa cikin ayyukan alheri. “Idan na yi alheri, zan shiga Aljanna; idan kuma na yi mummuna, wani wuri daban zan tafi – kamar can, ko ba haka ba?” ya faɗa wa Laura Ingraham na Fox News a bara.
A yanzu, shugaban yana jaddada cewa kawo zaman lafiya a Ukraine na iya zama mafi girman “kyakkyawan aiki” a rayuwarsa – ko ya kawo masa lambar yabo ta Nobel, nasarar siyasa, ko kuwa, kamar yadda ya yi raha, ya samu wuri a Aljanna.
