Featured
Girgizar Ƙasa Ta Yi Ajalin Mutum Sama Da 800 A Afghanistan
Sama da mutum 800 sun rasa rayukansu a Afghanistan bayan wata girgizar kasa mai karfin maki 6.0 da ta auku a daren Litinin, inda ta ruguza gidaje da dama. Hukumar Taliban ta tabbatar da cewa mutanen da abin ya shafa sun fi yawa a lardin Kunar, inda kuma fiye da 2,500 suka jikkata. Girgizar ta auku ne kafin tsakar dare, inda ta girgiza daga Kabul har zuwa Islamabad, babban birnin Pakistan.
Rahoton hukumar binciken kasa ta Amurka (USGS) ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 1.2 sun ji girgizar sosai, inda aka samu akalla girgizai na baya guda biyar a cikin daren. A Nangarhar an tabbatar da mutuwar mutum 12 da raunukan wasu 255, yayin da a Laghman kuma mutane 58 suka ji rauni. Wuraren da lamarin ya fi muni sun kasance cikin tsaunuka masu nisa, inda hanyoyi suka toshe, abin da ya sa agajin ya yi jinkiri.
Kungiyoyi da dama ciki har da Majalisar Dinkin Duniya sun shiga aikin ceto tare da hukumomin Taliban. Ma’aikatar tsaro ta tabbatar da aika fiye da jirage 40 domin kai dauki, yayin da mazauna yankuna ke kokarin bude hanyoyi. Wasu mazauna kauyukan sun bayyana cewa yara da mata suna ta ihu saboda tsoro, yayin da gidajen laka da yawa suka rushe gaba daya.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya mika sakon ta’aziyya tare da bayyana goyon baya ga jama’ar Afghanistan. Haka zalika, Paparoma Leo XIV ya bayyana bakin cikinsa kan wannan masifa da ta jawo asarar rayuka da dama. Wannan bala’i ya sake bayyana irin raunin gine-ginen kauyuka a kasar da ke cikin tsaunuka, inda talauci da koma bayan tattalin arziki suka kara tsananta radadin lamarin.
