Featured
Rikicin Tsaro: Matasa a Sokoto Sun Yi Barazanar Daukar Makamai Don Kare Kansu
Rikicin tsaro da ya addabi al’ummar Shagari a Jihar Sokoto ya sa matasan yankin suka nuna aniyarsu na shirin daukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga. A cikin wata sanarwa da dan gwagwarmayar matasa, Bello Bala Shagari, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis 04 ga Satumba, ya bayyana takaici kan abin da suka kira gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sun ce hare-haren da suka daɗe suna faruwa sun raba iyalai da muhallansu, sun durkusar da noma, tare da barin jama’a cikin tsananin fargaba.
Bello Shagari, jikan tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari, ya bayyana cewa matasan sun kai ga yanke shawarar “mataki na ƙarshe” na kare kansu da al’ummominsu sakamakon hare-hare da cin mutunci da ake yi musu. Ya ce matasan suna son zaman lafiya, amma rashin ganin matakin gwamnati ya tilasta musu tunanin ɗaukar doka a hannunsu.
Matasan sun roƙi Gwamnatin Jihar Sokoto da ta Tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro masu isasshen ƙarfi a Shagari da makotan ƙananan hukumomi. Sun jaddada cewa aikin gaggawa, ba alkawura kawai ba, shi ne zai dawo da kwarin gwiwa ya kuma hana al’ummar yankin fadawa cikin halin rikici. Sai dai masana tsaro sun yi gargadi cewa matakin daukar makamai na iya ƙara ta’azzara rikici da hana samun zaman lafiya.
