Connect with us

Featured

Zan Iya Barin Jam’iyyar NNPP – Abdulmumin Jibrin

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne idan ya bar jam’iyyar NNPP. Ya ce shi mutum ne da ya isa ya yanke shawara kan abin da ya fi masa amfani a siyasa, duk da cewa ya samu goyon bayan Kwankwasiyya wajen dawowa majalisa a 2023.

Jibrin ya ce ya shiga tafiyar Kwankwasiyya tun yana da kuɗi, kuma ya yi amfani da dukiyarsa wajen tallafawa jam’iyya, kamar yadda ita ma ta taimaka masa. Ya kara da cewa ba zai taɓa zagin Kwankwaso ba ko da zai bar NNPP, kamar yadda bai taba zagin Ganduje ba duk da rabuwarsu a baya.

Ya bayyana cewa yana da ’yancin canza jam’iyya zuwa kowacce – APC, PDP, ADC ko PRP – duk lokacin da ya ga dama. Sai dai ya tabbatar da cewa zai ci gaba da mutunta Kwankwaso a matsayin jagora, koda kuwa ba za su kasance a jam’iyya ɗaya ba.

Duk da kasancewarsa a NNPP, Jibrin na da kusanci da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya jagoranci kamfen dinsa a 2023 kafin ya koma NNPP. Ziyararsa ga Tinubu a makonnin baya ya tayar da jita-jita cewa shi da Kwankwaso na iya komawa APC nan gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahisholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet