Featured
Jam’iyyar NNPP Ta Kori Abdulmumin Kofa
Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da kin biyan kuɗin da ake buƙata na mambobi. Shugaban jam’iyyar a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan fitowar Jibrin a kafafen watsa labarai inda ya yi suka ga jam’iyyar da shugabancinta.
Dungurawa ya bayyana Jibrin a matsayin “ɗan siyasa marar ƙarfi” wanda nasararsa ta zabe ta samu ne kawai saboda kwankwasiyya da jamiyyar NNPP, ba ƙarfin kansa ba. Ya ce idan da karfi yake dashi, da ya ci zabe a APC tun da farko.
Shugaban ya ƙara da cewa an fara kafa kwamitin sulhu don sasanta matsalar bayan tattaunawarsa a Channels TV, amma daga baya ya sake yin magana da ta sabawa muradun jam’iyya, wanda hakan ya sa aka yanke shawarar korarsa. Haka kuma, ya zarge shi da kin biyan kuɗaɗen mambobi da doka ta jam’iyya ta wajabta, tare da bayyana cewa za su gurfanar da shi a kotu domin a dawo da kuɗin.
Dangane da jita-jitar cewa Jibrin zai koma APC, Dungurawa ya ce hakan ba zai shafi ƙarfin NNPP ba domin siyasa gamayya ce, kuma kwankwasiyya na nan da cikakken ƙarfi karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
