Featured
Adadin Mutanen Da Su Ka Mutu Sanadiyyar Gobarar Da Ta Faru a Ginin Afriland Towers a Lagos Ya Kai Mutum 10
An tabbatar da mutuwar karin mutane shida a gobarar da ta tashi a ginin kasuwanci na Afriland Towers mai bene shida da ke titin Broad a tsibirin Lagos. Wadanda suka rasu karin ma’aikatan kamfanin United Capital Plc ne da ke aiki a bene na uku da na hudu. Wannan ya kawo adadin mutanen da suka mutu a hatsarin zuwa 10, bayan hukumar FIRS ta tabbatar da rasuwar ma’aikatanta hudu a ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga ɗakin inverter da ke karkashin ginin da misalin ƙarfe 1:30 na rana a ranar Talata. Hakan ya jawo fitar hayaƙi mai kauri da firgitar mazauna ginin, inda aka ga wasu na ƙoƙarin tserewa ta tagogi. Hukumar kwana-kwana ta Tarayya, ta Jihar Lagos da sauran masu bada agajin gaggawa sun ceto mutane tara, inda aka farfado da biyar yayin da huɗu ke cikin mawuyacin hali.
Kamfanin United Capital Plc ya bayyana alhinin rasuwar ma’aikatansa shida tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan su da masoyansu. Kamfanin ya ce yana shirin gudanar da bikin tunawa don girmama rayuwar wadanda suka rasu tare da gode wa jami’an bada agaji da suka halarci wajen ceto jama’a.
Har yanzu hukumomin kwana-kwana da na bada agaji ba su fitar da sahihin adadin wadanda suka mutu ba, sai dai shaidu da wasu majiyoyi sun tabbatar “ba kowa ya tsira ba” a wannan mummunan lamari da ake kyautata zaton fashewar inverter ce ta haddasa shi.
