Addini
NAHCON Ta Buƙaci Maniyyata Su Fara Biyan Kudin Hajjin 2026
Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana damuwarta kan yadda maniyyata ke jinkirin biyan kudin Hajji, inda ta ce hakan yana iya kawo tsaiko wajen samun masauki mai kyau a Makkah da Madina. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh-Usman, ya bayyana haka ne a Katsina yayin da ya kai ziyara ga Gwamna Dikko Radda domin neman hadin kai a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma.
Farfesa Saleh-Usman ya bayyana wasu muhimman nasarorin da hukumar ta samu karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ciki har da tallafin naira biliyan 90 domin rage wa maniyyata nauyin sabon farashin kudin Hajji a 2024, da kuma naira biliyan 24 da aka biya don warware bashin jiragen sama na 2023, wanda ya ceci kamfanonin daga rugujewa. Haka kuma gwamnati ta shawo kan matsalar karbar kudin Hajji da katin kiredit da kuma yadda za a biya su a naira.
Hukumar ta kuma fadada tsarin ajiyar kudin Hajji tare da karin bankuna domin bai wa maniyyata damar tanadi a hankali, musamman matasa da masu karamin karfi. Saleh-Usman ya kara da cewa NAHCON ta mayar wa da jihohi kudi naira biliyan 5.3 kan ayyukan da ba a yi wa maniyyata na 2023 ba, abin da ya kara tabbatar da gaskiya da amana a harkar hajji.
A nasa jawabin, Gwamna Dikko Radda ya yi alkawarin hada kai da hukumar wajen wayar wa jama’a kai kan muhimmancin biyan kudin Hajji da wuri. Ya umurci Ma’aikatar Harkokin Addini ta jihar da Hukumar Jin Dadin Alhazai su cigaba da wayar da kai, tare da umartar malamai su yi amfani da hudubarsu wajen tunatar da jama’a kan muhimmancin yin rijista da wuri.
