Connect with us

Featured

Ƙungiyar Lauyoyi Ta Ƙalubalanci ‘Ƴan Sanda Kan Dokar Sanya Baƙin Gilashi a Mota

Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi tir da matakin rundunar ‘yan sanda na fara tilasta samun lasisin gilashin mota mai duhu (tinted glass permit), tana mai kiran tsarin “ba bisa doka ba.” Kungiyar ta ce za ta bayar da taimakon shari’a kyauta ga kowane ɗan ƙasa da aka ci zarafi a lokacin aiwatar da wannan doka. A cewar shugaban kwamitin ƙungiyar kan shari’o’in jama’a, Olukunle Edun (SAN), babu wata doka da ta bai wa ‘yan sanda ikon karɓar kuɗi ko sabunta lasisi, yana mai zargin wannan tsarin da neman tara kudaden shiga ne, ba tsaron jama’a ba.

NBA ta bayyana cewa lamarin yana gaban kotu, inda ta rubuta wa Sufeton ‘Yan Sanda wasika a ranar 2 ga Oktoba 2025, tana tunatar da shi cewa akwai ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1821/2025 a Babban Kotun Tarayya da ke kalubalantar sahihancin dokar. Kungiyar ta buƙaci ‘yan sanda su tsaya a matsayin da ake ciki har sai kotu ta yanke hukunci. Ƙarar ta nemi kotu ta ayyana dokar Tinted Glass Decree 1991 a matsayin ta sabawa kundin tsarin mulki, tare da hana ‘yan sanda ci gaba da tsare, tursasa ko karɓar kuɗi daga direbobi.

A cikin takardar, lauya Godspower Eroga ya zargi rundunar ‘yan sanda da niyyar karkatar da kudaden da za a tara ta hanyar wani asusun kamfani mai zaman kansa maimakon TSA. Ya kuma bayyana cewa dokar da ake amfani da ita ba ta fayyace ka’idojin tinted ba, kuma tana sabawa tsarin sabbin motocin zamani da ke zuwa da gilashi mai duhu daga masana’anta. Ya kara da cewa ko manyan jami’an ‘yan sanda suna amfani da motoci masu duhun gilashi ba tare da lasisi ba.

NBA ta yi Allah wadai da yadda aka kama motar wani alkali a Asaba a ranar farko ta aiwatar da doka, tana mai cewa hakan ya nuna hatsarin da tsarin ke tattare da shi. Kungiyar ta bayyana takaicinta kan yadda kotun hutu ta ƙi sauraron buƙatar dakatar da aiwatar da doka saboda dalilan tsaro. Ta jaddada cewa ya kamata kotuna su tsaya tsayin daka wajen kare jama’a da tsarin mulki, musamman a lokutan da irin wannan doka ke barazana ga ‘yancin al’umma.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet