Connect with us

Featured

Majalisa Na Duba Yiwuwar Ganin An Gudanar Da Zaɓen Shugaban Ƙasa, Gwamnoni Da Ƴan Majalisu a Rana Guda— Abbas

Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Tajudeen Abbas, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya himmatu wajen tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai fi na 2023 gaskiya da inganci. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin karɓar tawagar Tarayyar Turai (EU), inda ya ce Majalisar Dokoki ta ƙasa tana aiki kan gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 domin ƙara gaskiya da sahihanci a tsarin zaɓe na gaba.

Abbas ya ce sun tattara matsalolin da aka gano a zaɓen 2023 — musamman waɗanda masu sa ido na ƙasashen waje suka nuna — domin su yi gyare-gyare ta fuskar doka da tsarin mulki. Ya bayyana cewa majalisar dattawa da ta wakilai sun haɗu domin daidaita ra’ayoyi kan sauye-sauyen da ake shirin yi, kuma za su ware batun zaɓe a matsayin muhimmin abu guda domin amincewa da shi kafin ƙarshen watan Disamba.

Daga cikin sauye-sauyen da ake shirin yi akwai samar da kujeru na musamman ga mata da masu nakasa, da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, ‘yan majalisa, gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi a rana guda. Abbas ya ce wannan tsari zai taimaka wajen rage ɓata lokaci da ƙarfafa fitowar masu zaɓe. Ya kuma roƙi EU da ta taimaka wajen wayar da kan jihohi domin tabbatar da nasarar shirin.

Shugaban tawagar EU, Barry Andrews, ya yaba wa Majalisar Dokoki bisa ƙoƙarinta na ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya. A zaɓen 2023, kungiyoyin sa ido na cikin gida da na waje sun bayyana matsaloli irin su jinkirin isar kayan zaɓe, matsalolin BVAS, da tsaikon tura sakamako — lamarin da yasa gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da cewa zaɓen 2027 zai fi na baya inganci da sahihanci.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet