Featured
Zargi Kan Takardar Bogi: UNN Ba Ta Taɓa Ba Ni Takardar Digiri Ba – Minista
Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire na Najeriya, Uche Nnaji, ya amince cewa Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba. Wannan na zuwa ne bayan binciken shekaru biyu da jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar, wanda ya gano cewa takardun da ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu, Majalisar Dattawa, da wasu hukumomi, ba su fito daga jami’ar ba. Rahotanni sun nuna cewa tun bayan nadin sa a cikin jerin ministocin farko a watan Yuli 2023, ana tuhumarsa da mallakar takardun bogi.
A cikin shaidar da ya gabatar a kotu, Nnaji ya bayyana cewa an karɓe shi jami’a a 1981 don karatun Microbiology/Biochemistry, kuma ya kammala karatu a 1985, amma jami’ar ta ƙi ba shi takardar digiri saboda abin da ya kira rashin haɗin kai daga wasu jami’an makarantar. Duk da cewa jami’ar ta taba fitar da wata wasika a 2023 tana tabbatar da karatunsa, daga baya ta janye wannan ikirari, inda ta bayyana a hukumance cewa ba ya cikin jerin daliban da suka kammala karatu a 1985.
Wani jami’in jami’ar ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa bayan bincike, an gano cewa Nnaji bai taɓa kammala karatunsa ba. Ya ce, “Gaskiyar magana ita ce bai taɓa gama makaranta a nan ba. Fayil ɗinsa yana nan, yana nuna lokacin da ya daina zuwa karatu.” Wannan lamari ya ƙara tayar da tambayoyi kan yadda ya samu takardar digiri da ya gabatar wa hukumomin Najeriya, da kuma yadda ya samu damar yin NYSC.
Duk da irin wannan zargi, Nnaji bai amsa tambayoyin manema labarai ba tun lokacin da PREMIUM TIMES ta tuntuɓe shi a Janairu 2024. Har yanzu dai ana ci gaba da shari’a a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja, inda Nnaji ke neman kotu ta hana jami’ar UNN fitar da bayanan karatunsa ga kowa, tare da neman tilasta musu su mika masa takardun bayanan karatunsa.
