Addini
Tinubu Ya Umurci NAHCON Ta Sake Rage Kuɗin Aikin Hajji
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni ga Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 cikin gaggawa, tare da fitar da sabon farashin cikin kwanaki biyu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da wannan saƙo yayin wani muhimmin taro da shugabannin NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin. Wannan mataki ya biyo bayan rage kimanin Naira 200,000 da hukumar ta yi a baya kan farashin aikin Hajjin bara.
Shettima ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen tabbatar da fitar da sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. Ya kuma umarci masu ruwa da tsaki su gaggauta biyan kuɗaɗen da suka wajaba zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN), domin tabbatar da an kammala dukkan shirye-shirye cikin lokaci. Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya bayyana cewa wannan taron na nufin kammala dukkan shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, musamman batun farashin kujera.
A cewarsa, gwamnatin Tarayya na son rage wa maniyyata kuɗin tafiya la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa a yanzu. Ya bayyana cewa darajar naira tana ƙaruwa sakamakon gyare-gyaren gwamnati, don haka akwai buƙatar NAHCON ta yi amfani da sabon farashin canji na kasuwa wajen ƙididdige kuɗin. Hadejia ya ce idan aka aiwatar da wannan umarni, za a samu gagarumin ragi a kuɗin aikin Hajjin bana idan aka kwatanta da bara, inda maniyyata suka biya tsakanin Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6.
Shugabannin NAHCON da na jihohi sun nuna jin daɗinsu kan wannan umarni. Sakatare na NAHCON, Dakta Mustapha Mohammad, ya ce matakin zai ƙara yawan maniyyata saboda sauƙin farashi, yayin da Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya bayyana farin cikinsa, yana mai cewa matakin gwamnati zai sauƙaƙa wa al’umma wajen gudanar da wannan rukuni na addini.
