Connect with us

Featured

Trump Ya Cancanci Lambar Yabo Ta Jagoran Zaman Lafiya – Herzog

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya yaba wa Shugaban Amurka Donald Trump bisa rawar da ya taka wajen cimma yarjejeniya tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Herzog ya bayyana a shafinsa na X cewa “babu shakka Trump ya cancanci lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya” bisa wannan gagarumin ci gaba da ya kira dama ta sulhu, warkarwa da buɗe sabon babi na fata ga yankin.

Trump ne ya sanar da nasarar tattaunawar a Masar wadda ta samar da matsaya ta farko a shirin zaman lafiya na Amurka. Yarjejeniyar ta tanadi sakin dukkan mutanen da ake garkuwa da su a Gaza da kuma janyewar dakarun Isra’ila zuwa wani layi da aka amince da shi. Hamas ma ta tabbatar da amincewarta da wannan yarjejeniya.

A jawabin da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a New York kwanan nan, Trump ya ce tun bayan hawansa mulki a farkon shekarar nan ya riga ya kawo ƙarshen wasu rikice-rikice da dama a duniya, don haka ya kamata a ba shi lambar Nobel ta zaman lafiya.

Kwamitin Nobel zai bayyana wanda ya lashe lambar yabo ta bana a ranar Juma’a. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da yarjejeniyar zaman lafiya ta Gaza ke ƙara jawo hankalin duniya, inda Trump ke samun yabo daga wasu shugabanni da ƙasashe kan rawar da ya taka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet