Featured
Gwamna Mbah Zai Koma Jam’iyyar APC a Ranar Talata
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, zai sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a hukumance a ranar Talata, 14 ga Oktoba 2025, a birnin Enugu. Mbah zai shiga jam’iyya mai mulki tare da wasu ‘yan majalisar jiha da ta tarayya, mambobin zartarwa na jiha da shugabannin jam’iyya daga matakan mazabu da kananan hukumomi.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da Mataimakinsa na Kudu, Hon. Emma Eneukwu, sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen ƙarfafa tasirin jam’iyyar a yankin Kudu maso Gabas.
Shugaban rikon kwarya na APC a Jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya tabbatar da cewa za a karɓi Gwamna Mbah da mukarrabansa a cikin jam’iyyar a ranar da aka tsara. Wannan na zuwa ne bayan kwamitin aiki na ƙasa na APC ya rushe shugabancin jam’iyyar na jiha, tare da naɗa kwamitin rikon kwarya mai mutum bakwai.
Ana sa ran wannan sauyin sheƙa zai ƙara ƙarfafa matsayi da tasirin APC a yankin Kudu maso Gabas, musamman yayin da jam’iyyar ke shirin fadada goyon bayanta a jihohin yankin.
