Featured
Hukumar Kwastam Ta Sanya Ranar 14 ga Oktoba Don Gudanar Da Jarabawar Ƙarshe ta Ɗaukar Ma’aikata
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da cewa za a gudanar da jarabawar kwamfuta ta ƙarshe ga dukkan wadanda su ka yi nasarar zama Superintendent Cadre zuwa matakin ƙarshe a ranar Talata, 14 ga Oktoba, a fadin sassan ƙasar.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin sabunta bayanan daukar ma’aikata, an bayyana cewa za a gudanar da jarabawar ne lokaci guda a jihohin da aka ware bisa ga yankuna shida na ƙasar. Masu neman aikin za su shiga shafin hukumar ta https://updates.customs.gov.ng ta amfani da NIN domin ganin cikakkun bayanan jarabawarsu da cibiyoyin da aka ware musu, sannan su buga takardar shaidarsu ta shiga jarabawa.
Jihohin da za a gudanar da jarabawar sun haɗa da Lagos da Osun (Kudu maso Yamma), Enugu da Abia (Kudu maso Gabas), Rivers da Edo (Kudu maso Kudu), Abuja da Kwara (Tsakiya), Bauchi da Adamawa (Arewa maso Gabas), da kuma Kaduna da Sokoto (Arewa maso Yamma).
Hukumar ta gargadi masu neman aikin da su tabbatar sun halarci cibiyoyin da aka ware musu a kan lokaci, domin rashin halarta na iya haifar da soke cancanta. Haka kuma, ta ce za a ci gaba da fitar da karin bayanai da umarni ta shafin sabunta daukar ma’aikata na hukumar.
