Connect with us

Fashion

Maria Corina Ta Lashe Lambar Yabo Ta Zaman Lafiya Ta Nobel

An bai wa shugabar adawa ta Venezuela, Maria Corina Machado, lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta wannan shekara saboda jajircewarta wajen kare haƙƙin dimokuraɗiyya da kuma ƙoƙarinta na samar da sauyin mulki cikin lumana daga mulkin kama-karya zuwa dimokuraɗiyya. Kwamitin Nobel na Norway ya bayyana Machado a matsayin “fitacciyar jaruma mai ƙarfin hali a Latin Amurka,” duk da barazana ga rayuwarta, tana ci gaba da zama a cikin ƙasar tana jagorantar ƙungiyar adawa da aka dade ana danne ta ta hanyar maguɗin zaɓe da tsare-tsare na siyasa.

Machado ta shafe shekara guda tana ɓoye saboda matsin lambar gwamnati, inda ta zama abin koyi ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke neman sauyi. A lokacin da aka shirya zaɓen shugaban ƙasa a 2024, ita ce yar takarar adawa amma gwamnati ta hana ta tsayawa. Daga baya ta mara wa tsohon jakadan ƙasar, Edmundo Gonzalez Urrutia, baya domin ci gaba da fafutukar. Kwamitin ya ce Venezuela ta sauya daga ƙasa mai dimokuraɗiyya zuwa mulkin kama-karya da ya haifar da matsananciyar rikicin tattalin arziki, inda mutane kusan miliyan takwas suka bar ƙasar.

A gefe guda, shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke neman wannan lambar yabo, bai samu ba. Duk da ikirarin sa cewa ya cancanci lambar saboda rawar da ya taka wajen warware rikice-rikice, masana Nobel sun ce manufofinsa na “America First” sun saba da manufar lambar yabo ta zaman lafiya. Shugaban kwamitin Nobel, Jorgen Watne Frydnes, ya jaddada cewa ba sa yarda da matsin lamba ko kamfen na neman lambar yabo, sai dai suna bin ka’idar Alfred Nobel.

Lambar yabo ta Nobel tana zuwa da takardar girmamawa, kyautar kuɗi dala miliyan 1.2 da kuma zinariya. Za a gabatar da ita a Oslo a ranar 10 ga Disamba, ranar tunawa da rasuwar Alfred Nobel a 1896. A bana, lambar ta zo da mamaki domin ba a saka sunan Machado cikin masu sa ran lashewa ba, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin rawar da ta taka a fafutukar siyasa a Latin Amurka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet