Connect with us

Featured

Sabbin Dokokin CBN Na Iya Durƙusar Da Sana’ar POS

Sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar kan harkar agent banking na iya jefa kusan kashi 40 cikin 100 na masu amfani da na’urorin POS cikin wani yanayi. Shugaban ƙungiyar masu aikin POS (AMMBAN), Fasasi Sharafadeen, ya bayyana cewa sabon tsarin zai takaita harkokin kasuwanci, ya rage damar samun kuɗi a yankunan karkara, tare da barazana ga burin ƙasar na haɓaka shigar jama’a cikin tsarin kuɗi. CBN ta kafa iyaka ga kowanne mai POS na yin mu’amalar da bata wuce Naira miliyan 1.2 a rana ba, tare da tilasta su amfani da asusun da aka ware na musamman wajen gudanar da dukkan mu’amaloli. Haka kuma, an takaita kowanne abokin ciniki zuwa Naira dubu 100 a rana, tare da buƙatar na’urorin POS su kasance cikin wani takamaiman wuri (geofencing), domin hana amfani da su ba bisa ka’ida ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa shigar da tsarin “exclusivity” — wato tilasta kowanne mai POS ya yi aiki da kamfani guda ɗaya kacal — zai rage musu samun kuɗi da kuma jefa da dama daga cikinsu cikin mawuyacin hali. A cewarsu, yawancin masu POS na amfani da na’urori na dandamali daban-daban ne domin tabbatar da cewa abokan cinikinsu suna samun sabis mai inganci, musamman idan hanyar sadarwar wani kamfani ta samu matsala. Haka kuma, sabon tsarin ya haramta musu buɗe asusu da bayar da katunan ATM, da suke samun riba mai yawa daga gare su. Sharafadeen ya ce wannan mataki zai fi shafar ƙananan masu kasuwanci, musamman a yankunan da bankuna ba su da yawa.

A halin da ake ciki, wasu masu POS sun koka cewa iyakance mu’amaloli zuwa N1.2m a rana zai rage musu riba da kuma wahalar da ‘yan Najeriya wajen samun kuɗi a hannu. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa suna fitar da kuɗaɗe masu yawa a rana musamman lokacin kasuwa, kuma wannan sabon tsari zai rage musu adadin abokan ciniki da kuma ajiyar da suke tarawa. Wasu mata masu gudanar da POS a kasuwanni sun bayyana cewa wannan tsarin “ba adalci ba ne” domin shi ne ginshikin sana’arsu na tallafawa iyali.

Masana tattalin arziki sun bayyana ra’ayoyi mabambanta game da sabon tsarin. Tsohon daraktan CBN, Akpan Ekpo, ya ce manufar bankin na iya zama don inganta tsaro da rage yawan kuɗi a hannu, amma nasararta za ta dogara ne kan yadda za a aiwatar da tsarin yadda ya kamata. Haka kuma, masana daga Makarantar Kasuwanci ta Legas sun ce tsarin zai taimaka wajen gano masu zamba idan aka haɗa shi da BVN da TIN na masu POS. Sai dai wasu ƙungiyoyin masu hannun jari sun soki CBN da cewa tana tsoma baki fiye da kima a kananan harkoki, maimakon ta mai da hankali kan ayyukan asali kamar samar da takardun kuɗi masu tsafta da inganta ATM ɗin bankuna.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet