Connect with us

Featured

Rundunar Ƴansanda Ta Kama Ƴan Fashi 9 a Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaki da aikata laifuka, inda ta cafke wasu manyan ‘yan fashi guda tara tare da kwato mugayen makamai da motoci. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, a ranar Litinin, 13 ga Oktoba, 2025. Ya ce an kama wadanda ake zargin ne bisa umarnin IGP Kayode Egbetokun, bayan fashin da aka yi a unguwar Dorayi Babba, Kano.

An rawaito cewa, ‘yan fashin sun kai hari da misalin ƙarfe 2 na dare a ranar 8 ga Oktoba, inda suka kwace mota kirar Toyota Yaris, kudi kusan Naira miliyan 3.7, wayoyi guda uku da wasu kayayyaki, tare da jikkata matar gidan da suka kai wa harin. Rundunar ta kama mutum daya nan take, sannan ta cafke sauran takwas daga bisani a Kano da Kaduna ta hanyar rundunar Special Intervention Squad. Wadanda aka kama sun hada da matasa masu shekaru tsakanin 17 zuwa 24, kuma tuni duk su ka amsa laifukansu.

Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi guda uku, harsasai 18, wukake da adduna, fitilu, abin yankan ƙarfe, da mota kirar Toyota Corolla LE da ake amfani da ita wajen fashi. Kwamishinan ya ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike, tare da ci gaba da farautar sauran kayan laifi da abokan aikinsu.

Kwamishinan ya yabawa jami’an ‘yan sanda bisa jarumtarsu, tare da jinjinawa al’umma bisa hadin kai da bayar da bayanai. Ya kuma jaddada cewa shirin “Operation Kukan Kura” na rundunar ya taimaka matuka wajen rage fashi, sata da tada zaune tsaye a Kano, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai domin tabbatar da tsaro.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet