Connect with us

Addini

Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Laifin Yin Aure Ba Tare Da Amincewar Waliyyansu Ba

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa biyar, ciki har da amarya da ango, bisa zargin gudanar da auren bogi ba tare da amincewar iyayensu ba. Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano, ranar Litinin 13 ga Oktoba. Ya ce cikin wadanda aka cafke akwai wakilai biyu da shaidar aure daya, kuma hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa an kulla wannan aure ne da sadaki na Naira 10,000, wanda bai cika ka’idar da shari’ar Musulunci ta tanada ba. Aminuddeen ya bayyana cewa hakan ya sabawa tsarin aure na Musulunci da kuma doka, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci irin wannan take hakkin iyaye da karya doka ba.

Hukumar ta yi kira ga iyaye da su kara kulawa da harkokin zamantakewar ’ya’yansu, musamman a lamuran aure, domin kauce wa irin wannan sabawa doka da addini. Wannan mataki na hukumar na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Hisbah da ta fara shirye-shiryen auren gata na mutum 2,000, inda ake bukatar masu sha’awar shiga shirin su yi rajista tare da yin gwajin lafiya kafin a daura aure.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet