Connect with us

Addini

Gwamnan Jigawa Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukhmar Hisbah a Jihar

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu a kan kudirin dokar kafa Hukumar Hisbah ta jihar, wanda hakan ya mayar da ita hukuma mai zaman kanta, domin tabbatar da daidaito da tarbiyya a tsakanin al’umma.

Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi akan kudirin, a zaman majalisa da aka gudanar a baya-bayan nan, domin karfafa ayyukan hukumar Hisbah a fadin jihar.

Yayin bikin sanya hannu kan dokar da aka gudanar a ranar Talata 22 ga Yuli, a dakin taro na Gwamnatin Jiha da ke Dutse, yayin taron Majalisar Zartarwa na mako-mako, Gwamna Namadi ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar nasara da ta biyo bayan fiye da watanni takwas na aiki tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.

Ya ce, “A yau mun sanya hannu kan dokar kafa hukumar Hisbah, wadda ta maida hukumar hukuma a hukumance a jihar Jigawa.”

Ya kara da cewa, “Wannan wani tsari ne da muka fara tun watanni bakwai zuwa takwas da suka wuce, kuma a yau, da ikon Allah, mun kammala shi.”

Namadi ya bayyana fatansa cewa ayyukan hukumar Hisbah za su kawo karin daidaito da tsaftar tarbiyya a cikin al’umma.

Ya bukaci ma’aikatan Hisbah da su gudanar da ayyukansu da tsoron Allah, adalci da kishin aiki.

Gwamnan ya kuma yaba da kokarin kwamitin da ya duba kafa hukumar, inda ya ce sun nuna sadaukarwa da jajircewa wajen ganin kudirin ya zama doka.

Ya ce, “Kokarinsu ne ya taimaka wajen cimma wannan nasara.”

Gwamnan ya bayyana cewa, “Da rattaba hannu kan wannan doka, hukumar Hisbah yanzu tana da cikakken iko da karfi na aiki a fadin jihar Jigawa, bisa ga manufarta na samar da tarbiyya, adalci da jin dadin al’umma.

“Kafa hukumar a matsayin doka zai taimaka sosai wajen inganta ayyukanta da tabbatar da kyawawan dabi’u da adalci a cikin al’umma.”

Ya bayyana wannan mataki na gwamnati a matsayin alamar kudurin gwamnati na tabbatar da tarbiyya da daidaito a cikin al’umma, yana mai cewa aikinta zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabi’un jama’a.

Yayin karin bayani kan aikace-aikacen hukumar, Namadi ya ce, “Ayyukan hukumar sun hada da bayar da jagoranci na tarbiyya, tabbatar da adalci, da kuma inganta jin dadin al’umma.”

A karshe, ya bukaci jami’an hukumar Hisbah da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amana, domin tabbatar da cewa ayyukan hukumar na amfani da kuma inganci ga al’umma.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet