Connect with us

Featured

Birtaniya Ta Ware Dalar Amurka Miliyan 26.7 Domin Farfaɗo Da Gaza

Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana shirinsa na bayar da tallafin kuɗi domin taimaka wa gina yankin Gaza bayan shafe shekaru biyu ana yaƙi. A wani taron kasa da kasa da za a gudanar a birnin Sharm el-Sheikh na Masar, Starmer zai sanar da bayar da £20 miliyan (dalar Amurka miliyan 26.7) don gyara tsarin ruwa, tsafta da kiwon lafiya da ya lalace a yankin.

Starmer ya nufi Masar domin halartar taron zaman lafiya na Gaza, wanda shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi za su jagoranta, jim kadan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Ya ce wannan mataki ne na farko wajen kawo ƙarshen yaƙin, sannan mataki na gaba shi ne tabbatar da sake farfado da Gaza cikin gaggawa.

Gwamnatin Birtaniya ta kuma sanar da shirinta na shirya babban taro na kwanaki uku a Brinin Landan domin tsara dabarun farfado da Gaza bayan yaƙi da kuma tattauna sauye-sauye a hukumar gwamnatin Falasɗinu. Kasashe kamar Jamus, Italiya, Saudiyya, Jordan da hukumomin ci gaban ƙasa da ƙasa za su halarci taron, tare da kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari.

Ministar harkokin wajen Birtaniya, Yvette Cooper, ta ce Gaza ta lalace baki ɗaya sakamakon yaƙi, kuma wannan tallafi zai ba da damar ƙara ƙaimi wajen aikin jinkai da kuma samar da tsare-tsaren sake gina yankin. Ta ce Birtaniya za ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa ƙasashe da hukumomi, tare da amfani da ƙwarewar cibiyar kuɗin London don tallafawa aikin sake gina Gaza.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet