Connect with us

Addini

Bala Lau Da Pantami Za Su Halarci Taron Ƙungiyar Musulmin Najeriya a Birtaniya

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, zai gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na Nigeria Muslim Forum UK (NMFUK) da za a gudanar a birnin Manchester ranar Lahadi, 26 ga Oktoba. Taken taron na bana shi ne “Ethical Digital Economy: The Future of Community-Centred Islamic Digital Banking”, wato tattaunawa kan tattalin arzikin dijital bisa tsari da ɗabi’a a karkashin tsarin Musulunci.

Za a halarci taron da fitattun masana, manazarta, da kwararru a fannin fasaha da harkokin kuɗi, ciki har da Dr. Abdullahi Bala Lau, shugaban ƙungiyar JIBWIS (Izala), da kuma Mr. Raza Ullah, wanda shi ne shugaban kamfanin Pfida, cibiyar harkokin kuɗi ta ɗabi’a. Shugaban NMFUK, Dr. Bilyaminu Romo, ya ce taron zai zama dandamali na musayar ilimi, girmama al’adu, da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma.

Dr. Romo ya bayyana cewa tattaunawar za ta mayar da hankali kan yadda ka’idojin Musulunci za su iya jagorantar kirkire-kirkire a harkokin kuɗi na zamani, musamman wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da ci gaban kowa. A cewarsa, taken taron yana nuna jajircewar kungiya wajen gina tsarin tattalin arziki mai ɗorewa da ya haɗa mutane baki ɗaya.

Ana sa ran Farfesa Pantami zai bayyana rawar da fasahar zamani za ta taka wajen faɗaɗa damar samun kuɗin Musulunci a Najeriya, wadda masana ke kimanta darajar kasuwarta sama da dala biliyan huɗu. Baya ga batun kuɗi, taron zai tattauna kan haɗin kai, fahimtar juna tsakanin al’ummomi, da kuma yadda ake iya haɗa kai wajen ƙarfafa ƙimomin tausayi da hidima ga al’umma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet