Connect with us

Featured

Ma’aikatan Jinya 15,421 Ne Su Ka Bar Najeriya Zuwa Birtaniya Cikin Shekaru Takwas – Rahoto

Akalla malaman jinya da ungozoma 15,421 da aka horar a Najeriya ne aka yi wa rajista domin su yi aiki a Birtaniya (UK) tsakanin shekarar 2017 zuwa 31 ga Maris, 2025, in ji sabon rahoto daga Hukumar Rajistar Ma’aikatan Jinya da Haihuwa ta UK (NMC).

Wannan hukuma ce ke da alhakin rajistar kwararrun ma’aikatan jinya da haihuwa da kuma bincike kan korafe-korafe da suka shafi aikinsu a Birtaniya.

A cewar rahoton, daga 30 ga Satumba, 2024, adadin ya kasance 14,815, amma ya karu zuwa 15,421 a ranar 31 ga Maris, 2025 – karin kashi 4.1 cikin 100 a cikin watanni shida.

Rahoton ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta uku mafi yawan nurses da suka je UK, bayan Philippines da India.

A cikin shekarar da ta gabata kadai, ma’aikatan lafiya 20,671 daga wajen UK ne suka shiga rajistar NMC a karon farko. Wannan adadi ya ragu da kashi 30.2 cikin 100 idan aka kwatanta da 29,628 da suka shiga a shekara ta baya (Maris 2024).

Ana ganin wannan raguwar ta shafi kasashen India, Philippines da Najeriya.

Wadanda suka fito daga India sun ragu da kashi 36.7%

Philippines – 47.6%

Najeriya – 25.5%

Bugu da ƙari, an fitar da 5,276 ma’aikata daga waje daga cikin rijista a wannan lokaci – karin kashi 33.3% idan aka kwatanta da 3,959 na shekarar da ta gabata.

Sai dai, NMC ta ce wannan yana da nasaba da yawan masu rijista da ke karuwa – kashi 2.7% daga cikin kwararrun na kasa da kasa ne suka fita, idan aka kwatanta da kashi 2.4% a bara. Daya daga cikin dalilan hakan na da alaka da canje-canje a tsarin izinin aikin lafiya da kula (Health and Care Worker visa).

Hakanan, gwamnatin Ingila ta kara mayar da hankali kan daukar ma’aikata daga cikin gida karkashin tsarin NHS Long Term Workforce Plan.

Wani bincike da Health Foundation ta gudanar ya gano cewa yawan masu neman barin UK zuwa wasu kasashe na kara yawa, musamman saboda burin samun albashi mafi girma.

Rahoton ya kara da cewa duk da karuwar wadanda aka horar a cikin UK da ke shiga rijista, wannan karuwar ba ta wadatar wajen maye gurbin raguwar daukar ma’aikatan daga waje ba. Saboda haka, yawan sabbin masu rijista a shekara ya fara raguwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet