Featured
Ganawarmu Da Putin Za Ta Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine – Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana fatan ganawar da aka shirya tsakaninsa da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, a birnin Budapest na ƙasar Hungary, za ta zama mataki na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Firaiministan Hungary, Viktor Orban, ya tabbatar da cewa an riga an fara shirye-shiryen wannan muhimmin taro, bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Mista Trump.
A yau ne kuma ake sa ran Trump zai gana da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, a Fadar White House. Ana kyautata zaton Zelensky zai sake roƙonsa ga Trump da ya amince Amurka ta sayar wa ƙasarsa makaman linzami masu kai dogon zango — waɗanda za su iya kai farmaki cikin ƙasar Rasha.
Sai dai rahotannin daga Amurka na nuna cewa Rasha na iya yin ƙoƙari ta jan ra’ayin Trump kada ya amince da wannan bukata. Fadar Kremlin ta bayyana cewa Putin ya gargadi Trump cewa irin wannan mataki na iya jefa dangantakar Rasha da Amurka cikin mawuyacin hali.
