Connect with us

Featured

Kwastam Ta Kama Wasu Motoci Dauke da Lita 120,000 na Man Fetur a Sokoto

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kama manyan motoci guda biyu dauke da jimillar lita 120,000 na man fetur da ake zargin an karkatar daga inda aka nufa da su. Kwamandan Ayyukan Musamman na Operation Whirlwind a Yankin B, Kola Olawole, ne ya bayyana haka a Sokoto, inda ya ce an kama motocin ne a kan titin Sokoto–Illela ranar 4 ga Oktoba. Motar farko da ta ɗauki lita 60,000 da ta biyu mai lamba DKA 309 XA da GSW 321 XA an gano sun karkata daga Kano zuwa Sokoto don fitar da man ta hanyar Ilela.

Olawole ya ce direbobin motocin sun tsere bayan jami’an kwastam sun yi ƙoƙarin cafke su. Bincike ya nuna cewa an karkatar da man ne domin fasa ƙwauri ta iyakar Illela, lamarin da ya saba wa ka’idojin jigilar man fetur da dokokin ƙasa. Ya bayyana cewa irin wannan karkatarwa ba wai laifin tattalin arziki ba ne kawai, har ma barazana ce ga tsaron makamashi da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Kwamandan ya kara da cewa aikin Operation Whirlwind ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile fasa ƙwaurin man fetur a yankuna daban-daban, abin da ya taimaka wajen daidaita rabon mai a cikin ƙasar. Ya ce hukumar za ta ci gaba da tsaurara matakai don hana masu satar albarkatun ƙasa cutar da tattalin arzikin ƙasa.

An mika motocin da aka kama ga Ali Ajimi, wanda shi ne mai kula da hukumar NMDPRA a yankin Sokoto/Kebbi, domin ci gaba da bincike da daukar matakan doka. Kwastam ta sha alwashin cigaba da kai farmaki kan masu fasa ƙwauri da masu karkatar da kayayyakin gwamnati.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinovdcasinoholiganbetmarsbahissahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet