Connect with us

Featured

Yajin Aiki: Ranar Litinin Muke Tsammanin Martanin Gwamnatin Tarayya – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana cewa tana sa ran samun amsar gwamnatin tarayya a ranar Litinin, yayin da yajin aikin gargadi na makonni biyu ya shiga rana ta shida. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja, inda ya ce har yanzu ba a samu wani sabon mataki daga Ma’aikatar Ilimi ba.

Wannan na zuwa ne bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, ya tabbatar da cewa majalisar za ta shiga tsakani domin dakile rikicin daga ƙara ta’azzara. ASUU ta shiga yajin aiki ne bayan ƙarewar wa’adin gargadi ga gwamnatin tarayya a ranar Lahadin makon da ya gabata, bisa matsalolin da suka shafi yarjejeniyar 2009 da batutuwan albashi da tallafin jami’o’i.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi, tare da fitar da N50bn don biyan hakkokin malaman jami’a da kuma saka N150bn a kasafin 2025 domin farfaɗo da jami’o’i. Sai dai ASUU ta ce ba ta ga wani gagarumin mataki da zai sa ta dakatar da yajin aikin ba.

ASUU na neman kammala yarjejeniyar 2009 da gwamnatin tarayya, sakin albashin watanni uku da rabi da aka hana, da samar da ingantaccen kuɗi ga jami’o’in gwamnati, da dakatar da gallazawa malaman wasu jami’o’i. Haka kuma suna neman biyan bashin albashi da na haɓakar matsayi da kuma kuɗaɗen da aka cire daga ƙungiyoyi ba tare da tura su ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet