Connect with us

Featured

Tinubu Ya Naɗa Sabon Minista

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya mika sunan Dr. Bernard Doro daga Jihar Filato ga Majalisar Dattawa domin tantancewa a matsayin sabon Ministan Tarayya. Naɗin nasa ya biyo bayan saukar Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsohon Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, wanda yanzu ya zama Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan bayanai da dabarun sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata 21 ga Oktoba. A cewar sa, shugaban ƙasar ya yanke shawarar cike guraben ministoci biyu da suka rage a majalisar zartarwa, ciki har da na Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira wanda ya ajiye aikinsa makonnin da suka gabata.

An haifi Dr. Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969 a garin Kwall, Ƙaramar Hukumar Bassa, Jihar Filato. Ya na da gwaninta mai zurfi na fiye da shekaru 20 a fannoni daban-daban da suka haɗa da aikin likitanci, kula da harkokin magunguna, shugabanci, da ci gaban al’umma a Najeriya da Birtaniya.

Ya na da digiri a fannin Pharmacy da Law, MBA kan dabarun kasuwanci masu dogaro da fasaha, da kuma Master’s a Advanced Clinical Practice. Haka kuma, Doro ya taka rawa wajen shiryawa da tallafa wa matasa a Najeriya da ƙasashen waje, wanda hakan ya ƙara masa suna a fagen hidimar jama’a. Idan aka tabbatar da nadinsa, zai shiga cikin majalisar ministocin Tinubu a taron FEC mai zuwa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet