Featured
Paul Biya Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasar Kamaru Karo Na Takwas
Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na takwas a jere, kamar yadda Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta tabbatar. Biya, wanda ke da shekara 92, ya samu nasarar ne da kashi 53.66% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen da aka gudanar a baya-bayan nan.
Wannan nasara na nufin shugaban zai ci gaba da jagorantar ƙasar Kamaru har zuwa shekara ta 2032, lamarin da ya ƙara tsawaita mulkinsa wanda ya fara tun daga shekarar 1982. Hakan ya tabbatar da shi a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi dade suna mulki a nahiyar Afirka.
A sakamakon zaɓen, jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya zo na biyu da kashi 35.19% na ƙuri’un da suka haura miliyan ɗaya. Duk da haka, jam’iyyarsa ta bayyana cewa za ta duba yiwuwar ƙalubalantar sakamakon saboda zargin wasu matsaloli da suka shafi tafiyar da zaɓen.
Rahotanni sun nuna cewa, duk da tsananin shekaru da jinkirin motsi, Paul Biya ya ci gaba da samun goyon bayan manyan jam’iyyun ƙasa da kuma sassan tsaron Kamaru, wanda hakan ya ƙara ƙarfafa matsayinsa a siyasar ƙasar.
